BABBAR MATSALAR MAZAJENMU A YANXU
[BABBAR MATSALAR MAZAJENMU A YANXU]. Abun ya wuce misali, domin babban matsalan mazajen auranmu yanxu shine neman mata tare da zina,Abun ya zama ruwan dare a wannan zamanin namu, kaga namiji magidanci yana aikata zina ba a tare da kunya ba ko tsoron Allah, wanda akalla wacce zaki ga yana nema basu wuce sa'o'in 'ya'yansa, kalilan dinsune suka tsaya Kawai akan soyayya kawai da 'yan mata ba tare da sun yi zina dasu ba, wani ma zaki ga da wacce ba musulma ba yake yi, wanda hakan ke jawo mana raini a wurinsu. Baki tabbatar da maganar da nake fada sai kina jami'a, a kullun dare zaki ga motoci sun kusa hamsin a fake a bakin hostel anzo wurin 'yan mata wanda akasarinsu masu iyali ne, wani har da jikoki da surukai,zaki gansu bakin ramat hostel(b.u.k kano) ko Queen Amina(A.b.u zaria) kowanne tare da budurwarsa anan zasu gama shafe² da tsotse² yaran mutane, wani hatta zina ma zaiyi da budurwar a cikin mota, ko kuma ya kaam hotel ya kaita can, wa'iyazubillah😢😢. ...